20 Faburairu 2017 - 12:26
Iran: Ba Mamaki Don An Sami Haduwar Baki Tsakanin Saudiyya Da Isra'ila Kan Iran

Kakakin Ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran Bahram Qassemi ya bayyana cewar matsaya guda da aka samu tsakanin Saudiyya da haramtacciyar kasar Isra'ila kan Iran ba abin mamaki ba ne don kuwa ba haka siddan lamarin ya faru ba.

Kakakin Ma'aikatar harkokin wajen na Iran ya bayyana hakan ne yayin da yake mayar da martani ga baki guda da aka samu tsakanin ministan harkokin wajen Saudiyya da ministan yakin haramtacciyar kasar Isra'ilana jawabin da suka gabatar a mabanbantan lokuta a wajen taron harkokin tsaro na Munich na kasar Jamus kan Iran inda ya ce akwai karfafan dalilai da suke nuni da cewa akwai alaka ta kut da kut da kuma hadin gwiwa tsakanin Saudiyya da Isra'lan.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen na Iran ya kara da cewa a halin yanzu Saudiyya da H.K.Isra'ila suna kokari ne wajen hada  wani kawance na kasa da kasa don fada da Iran sakamakon shan kashin da suke ci gaba da fuskanta kan lamurra daban-daban a yankin Gabas ta tsakiya.

A jawabin da suka gabatar a wajen taron na Munich, ministan harkokin wajen Saudiyya Adel Al-Jubair da ministan yakin haramtacciyar kasar Isra'ilan Avigdor Lieberman sun zargi Iran da goyon bayan ayyukan ta'addanci alhali kuwa a fili yake cewa Saudiyya ita ce kan gaba wajen goyon bayan kungiyoyin 'yan ta'addan irin su ISIS da sauransu lamarin da kasashen duniya da dama sun tabbatar da hakan.288